Mali : An Kai Hari Shalkwatar Rundinar G5 Sahel
Rahotanni daga Mali na cewa a kalla mutane 6 suka rasa rayukansu, a wani hari da aka kai a shelkwatar rundinar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci ta G5 Sahel, dake birnin Sevare a tsakiyar Mali.
Ganau da kuma da majiyoyin tsaro sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, an samu fashewar wani abu, kafin daga bisani an yi ta musayar huta.
Bayanai sun ce wani dan kunar bakin wake ne da ya nemi kusa kai cikin shelkwatar ta G5 Sahel, ya kai harin, wanda shi ne irinsa na farko da aka taba kai wa a cibiyar rundinar ta hadin guiwar kasashen na gungun G5 Sahel da suka hada da (Mali, Burkina Faso, Nijar, Mauritania da kuma Chadi) , wacce aka kaddamar da ita a cikin shekara 2017 data gabata don yaki da ta'addanci.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki uku kafin wata ganawa da aka tsara yi a birnin Nouakchott, a daura da taron kungiyar tarayya Afrika ta (AU), karo na 31 a kasar Mauritania, tsakanin Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kuma takwarorinsa na kasashen gungun kungiyar ta G5 Sahel.