Boko Haram Ta Kashe Sojojin Nijar 10
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32158-boko_haram_ta_kashe_sojojin_nijar_10
Hukumomin tsaro a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar sojojin kasar 10 da kuma batar wasu 4, da kuma uku da suka raunana, bayan wani hari da aka kai masu a yankin Diffa a kusa da tafkin Chadi.
(last modified 2018-08-22T11:32:03+00:00 )
Jul 02, 2018 10:18 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Sojojin Nijar 10

Hukumomin tsaro a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar sojojin kasar 10 da kuma batar wasu 4, da kuma uku da suka raunana, bayan wani hari da aka kai masu a yankin Diffa a kusa da tafkin Chadi.

Harin wanda ake danganta wa daga kungiyar Boko haram, an dai kai shi ne a cikin daren ranar Asabar data gabata a kauyen Bla Brin, dake nisan kilomita 40daga birnin N'Guigmi a kusa da yankin tafkin Chadi.

Mayakan sun kuma kone motocin soji masu yawa kafin su arce, kamar yadda kakakin ma'aikatar tsaron kasar,  Kanal Abdul-Aziz Touré, ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.