Somaliya : Harin Al'Shebab Ya Kashe Mutum 5 A Ma'aikatar Tsaro
(last modified Sat, 07 Jul 2018 15:59:54 GMT )
Jul 07, 2018 15:59 UTC
  • Somaliya : Harin Al'Shebab Ya Kashe Mutum 5 A Ma'aikatar Tsaro

'Yan sanda a Somaiya sun ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu awasu jerin hare hare da kungiyar Al'shebab ta kai a ma'aikatar tsaro kasar dake Mogadisho babban birnin kasar.

Da yake sanar da hakan kwamandan 'yan sanda birnin Ibrahim Mohamed, ya ce an kai hari biyu ne aka kai a ma'aikatar tsaron kasar dake kusa da majalisar dokoki.

Bayanai daga kasar sun kuma ce an bude wuta, bayan kaddamar da hare haren, kuma dukkan mutane 5 da lamarin ya rusa dasu fararen hula ne, sai kuma wasu sama da 10 da suka raunana.

A cikin wata sanarwa data fitar kungiyar 'yan Al'shabab dake ikirari da sunan jihadi, dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaïda, ta ce ita ce keda alhakin kai harin.

Kungiyar Al'shabab dai ta sha alwashin ganinbayan gwamnatin kasar ta Somaliya, dake samun goyan bayan kasashen duniya, da kuma dakaru 20,000 na tawagar kungiyar tarayya Afrika (Amisom).