An Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Mali
A Mali, yau Asabar ce aka fara yakin neman zamen shugaban, inda 'yan takara 24 zasu fafata a zaben na ranar 29 ga watan nan na Yuli da muke ciki.
Shugaban kasar mai ci Ibarhim Bubakar Keita na daga cikin 'yan takara dake fafatawa a zaben.
A yayin yakin neman zaben da za'a kwashe kwanaki 21 ana yi, 'yan takarar zasu fayyace manufofinsu na siyasa, ga 'yan kasar miliyan takwas da suka cancanci kada kuri'a.
Saidai babban kalubalen dake gaban 'yan takara shi ne yadda zasuyi yakin neman zaben a wasu sassan kasar dake fama da matsaloli na tsaro, da suka hada da arewaci da kuma tsakiyar kasar.
Baya ga hakan kuma akwai matsalar raba katin zabe, inda kawo yanzu bayanai ke cewa kashi 15% ne kawai na masu zabe suka karbi katinsu.