Tunisia : Harin Ta'addanci Ya Kashe Jami'an Tsaro 6
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32244-tunisia_harin_ta'addanci_ya_kashe_jami'an_tsaro_6
Hukumomi a Tunusiya sun ce an kashe wasu jami'an tsaron kasar shida a wani harin ta'addanci da aka kai masu a yankin arewa maso yammacin kasar a wannan Lahadin.
(last modified 2018-08-22T11:32:04+00:00 )
Jul 08, 2018 16:18 UTC
  • Tunisia : Harin Ta'addanci Ya Kashe Jami'an Tsaro 6

Hukumomi a Tunusiya sun ce an kashe wasu jami'an tsaron kasar shida a wani harin ta'addanci da aka kai masu a yankin arewa maso yammacin kasar a wannan Lahadin.

 Bayanai sun wannan dai shi ne hari mafi muni a kasar a cikin sama shekaru biyu.

Wata nakiya ce ta tarwaste inda ta kashe jami'an na gardi tsarki shida a kusa da iyaka da kasar Aljeriya, a lardin Ain Sultan, a yankin Jenduba, a cewar yadda wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gidan kasar.

Waki kakakin ma'aikatar wanda ya sanar da mutuwar jami'an tsaro 8 tun da farko, ya ce 'yan ta'addan sun bude wa sojojin wuta bayan tashin nakiyar.

Tuni dai aka shiga farautar 'yan ta'addan, a cewar jami'in.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai an fi nuna 'yar yatsa ga kungiyoyin nan dake ikirari da sunan jihadi da suka hada da kungiyar Al'qaida a yankin kasashen larabawa na Maghreb, da kuma kungiyar Jund al Khaifa dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.