Kungiyar Al'qa'ida Ta Dauki Nauyin Kai Hari A Kasar Tunisiya
Jaridar al-kudsu al-arabi ta ambato rundunar da take kiran kanta Uqbatu Bin Nafiu mai alaka da al-qa'ida tana cewa ita ce ta kashe sojojin kasar a jiya lahadi
Harin na jiya lahadi wanda aka kai akan dakarun tsaron kasar Tunisiya da suke sintiri a yankin Saraya a ke Garul-Dimaa, ya yi sanadin mutuwar tara daga cikinsu.
Rundunar Unqbatu Bin Nafiu ta fara kai hari ne a watan Disamba na 2012 a gundumar al-Qasrin a yamacin kasar Aljeriya.
Rundunar Uqbatu Bin Nafiu ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Tunisiya.
Tun daga 2011 zuwa yanzu ana samun kai hare-haren ta'addanci a fadin kasar ta Tunisiya. Da akwai 'yan kasar Tunisiya fiye da 5000 da suka yi yaki a kasashen Iraki da kuma Syria a karkashin kungiyoyin 'yan ta'adda na Al'qaeda da kuma Da'esh.