Kungiyar Al'qa'ida Ta Dauki Nauyin Kai Hari A Kasar Tunisiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32255-kungiyar_al'qa'ida_ta_dauki_nauyin_kai_hari_a_kasar_tunisiya
Jaridar al-kudsu al-arabi ta ambato rundunar da take kiran kanta Uqbatu Bin Nafiu mai alaka da al-qa'ida tana cewa ita ce ta kashe sojojin kasar a jiya lahadi
(last modified 2018-08-22T11:32:05+00:00 )
Jul 09, 2018 11:58 UTC
  • Kungiyar Al'qa'ida Ta Dauki Nauyin Kai Hari A Kasar Tunisiya

Jaridar al-kudsu al-arabi ta ambato rundunar da take kiran kanta Uqbatu Bin Nafiu mai alaka da al-qa'ida tana cewa ita ce ta kashe sojojin kasar a jiya lahadi

Harin na jiya lahadi wanda aka kai akan dakarun tsaron kasar Tunisiya da suke sintiri a yankin Saraya a ke Garul-Dimaa, ya yi sanadin mutuwar  tara daga cikinsu.

Rundunar Unqbatu Bin Nafiu ta fara kai hari ne a watan Disamba na 2012 a gundumar al-Qasrin a yamacin kasar Aljeriya.

Rundunar Uqbatu Bin Nafiu ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Tunisiya.

Tun daga 2011 zuwa yanzu ana samun kai hare-haren ta'addanci a fadin kasar ta Tunisiya. Da akwai 'yan kasar Tunisiya fiye da 5000 da suka yi yaki a kasashen Iraki da kuma Syria a karkashin kungiyoyin 'yan ta'adda na Al'qaeda da kuma Da'esh.