Zimbabwe : 'Yan Adawa Na Zanga zanga Kan Yunkurin Magudi a Zabe
(last modified Wed, 11 Jul 2018 17:09:20 GMT )
Jul 11, 2018 17:09 UTC
  • Zimbabwe : 'Yan Adawa Na Zanga zanga Kan Yunkurin Magudi a Zabe

A Zimbabwe, dubban magoya bayan jam'aiyyun adawa ne suka ne suka gudanar da wata zanga-zanga yau Laraba a Harare babban birnin Kasar, domin jan kunnen gwamnatin kasar akan duk wani yunkurin tafka magudi a zaben kasar dake tafe.

A ranar 30 ga watan Yulin nan ne za'a gudanar da manyan zabukan kasar ta Zinbabwe, wadanda su ne na farko tun bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya mika mulki bisa matsin lambar sojoji da jam'iyyarsa ta Zanu PF mai mulki.

Jagoran jam'iyyar MDC data kira zanga zangar, Nelson Chamisa, ya fada wa masu aiko da rahotanni cewa, suna bukatar a gudanar da sahihin zabe a kasar, don kuwa ba zasu shiga zaben da basu san yadda aka shirya shi ba, don haka suna bukatar samun daidaito tsakaninsu da gwamnatin kan yadda za'a shirya zaben.

A baya bayan dai ana ta korafi kan jaddawalin zaben kasar ta Zimbabwe, wanda aka ce yana cike da kura kurai tun a lokacin tsohon shugaban kasar Mugabe.

Shugaban kasai mai ci, Emersom Managwagwa dai ya sha nanata alkawarin cewa, za'ayi adalci a zabukan kasar dake tafe da suka hada da na shugaban kasa da 'yan majalsiar dokoki.