Wasu 'Yan Ta'adda Sun Yi Yunkurin Kai Hari Fadar Shugaban Kasar Somaliya
Wasu motoci biyu sun tarwatse a kusa da fadar shugaban kasar Somaliya a kokarin da wasu gungun 'yan ta'adda suka yi na kai hari kan fadar shugaban kasar a yau Asabar.
Majiyar rundunar 'yan sandan Somaliya ta sanar da cewa: 'Yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ta Somaliya sanye da kakin soji sun yi yunkurin kai harin wuce gona da iri kan fadar shugaban kasar da ke birnin Magadishu da wasu motoci biyu makare da bama-bamai, inda jami'an 'yan sandan kasar suka bude musu wuta lamarin da ya janyo tarwatsewar motocin tare da halakar 'yan ta'adda guda uku.
Har ila yau tarwatsewar motocin biyu sun janyo hasarar rayukan 'yan sandan gwamnatin kasar uku tare da jikkatan wasu fararen hula akalla bakwai.
Harin na yau Asabar ya zo ne bayan mako guda da wani hari da 'yan kungiyar ta Al-Shabab suka kai kusa da ma'aikatar ministan harkokin cikin gidan kasar Somaliya da ke birnin Mogadishu, inda suka kashe mutane akalla tara.