Ministan Kare Hakkin Bil'adama Na Kasar Tunisia Ya Yi Murabus.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32331-ministan_kare_hakkin_bil'adama_na_kasar_tunisia_ya_yi_murabus.
Ministan kare hakkin bil'adama na kasar Tunisia Mahdi bin Garbiyya ya ajiye mukaminsa tare da nuna damuwarsa kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati a kasar.
(last modified 2018-08-22T11:32:06+00:00 )
Jul 15, 2018 07:04 UTC
  • Ministan Kare Hakkin Bil'adama Na Kasar Tunisia Ya Yi Murabus.

Ministan kare hakkin bil'adama na kasar Tunisia Mahdi bin Garbiyya ya ajiye mukaminsa tare da nuna damuwarsa kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati a kasar.

Tashar talabijin ta al-alam a nan Tehran ta bayyana cewa Mahdi Gharbia ya mikawa Priministan kasar ta Tunisa Yusuf Shahid bukatar ajiye aikin nasa ne a jiya ya kuma amince. 

A wani fefen Vedio wanda ya watsa a cikin shafinsa na Facebook Mahdi Gharbia ya bayyana cewa ya ajiye aikin na sa ne don kare mutuncinsa da kuma'yencinsa wanda ya sabawa wasu lamura a gwamnatin Yusuf Shaahid da bai amince da su ba. 

Masu adawa da gwamnatin Yusuf Shaahid dai suna ganin gwamnatinsa ta gaza a fagen raya tattalin arzikin kasar. Sannan jam'iyyar Nida wacce ita ce ta dora Yusuf Shaahid kan kujerar Priministan kasar ta Tunisi, itama ta shiga cikin wadanda suke sukan gwamnatinsa da gazawarta.