Ran Gadin Ministar Tsaron Faransa A Yankin Sahel
(last modified Sat, 21 Jul 2018 05:47:19 GMT )
Jul 21, 2018 05:47 UTC
  • Ran Gadin Ministar Tsaron Faransa A Yankin Sahel

A ci gaba da ran gadin da take a yankin Sahel domin karfafa wa kungiyar G5 Sahel, kan yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi, ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta isa a birnin Ouagadugu na kasar Burkina Faso.

Madame Parly, ta gana da shugaban kasar ta Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, inda ta jadadda masa da goyan bayan Faransa ga rundinar hadin guiwa ta gungun kasashen G5 Sahel.

Burkina Faso na daga cikin kasashe biyar na yankin Sahel da suka hada da Mali, Nijar, Chadi da Mauritania da suka kafa rundinar soji ta tsakaninsu da zata yaki ta'addanci.

Kafin Burkina Faso ministar tsaron ta Faransa ta kai irin wannan ziyara a Jamhuriya Nijar, inda ta gana da shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu wanda shi ne yake rike da shugabancin kungiyar ta G5 Sahel a wannan karo.

A Jamhuriyar ta NIjar, bangarorin sun jadadda ganin rundinar ta samu kayan aiki da tallafi ta yadda zata shiga aikinta gadan-gadan.