An Kashe Direbobin Taxi 11 A Afirka Ta Kudu
Kakakin 'yan sandar Kasar Afirka ta kudu ya sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wata karamar Bas dauke da Direbobin Taxi tare da hallaka 11 daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto kakakin jami'an tsaron 'yan sanda na kasar Afirka ta kudu na cewa a daren jiya assabar wasu mutane dauke da makamai sun kaiwa wata karamar Bas dake dauke da Direbobin Taxi hari a yayin da suka fito daga garin Kvasoul-Natal-a kan hanyarsu ta komawa Johannesburg, inda suka kashe 11 daga jikinsu tare da jikkata wasu 4 na daban.
Kakakin 'yan sandar Afirka ta Kudu ya yi ishara da cewa mutanan da aka kashe 'yan kungiyar kwadago ne na Gauteng sannan ya ce mutanan wannan yanki suna tsananin kiyaya da direban Taxi, amma dai a halin yanzu jami'an 'yan sanda na gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta'addanci.