Kungiyar Brics Ta Fara Taron Kwanaki Biyu A Afirka Ta Kudu
(last modified Tue, 24 Jul 2018 19:06:29 GMT )
Jul 24, 2018 19:06 UTC
  • Kungiyar Brics Ta Fara Taron Kwanaki Biyu A Afirka Ta Kudu

kasashen duniya masu samun habakar tattalin arziki wato Brics sun fara gudanar da taronsu na shekara shekara a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a wannan talala hukumomin kasashen biyar masu samun habakar tattalin arziki da ake kira Brics sun fara gudanar da taron kwanaki biyu a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, inda a cikin kwanaki biyu za su canza miyau kan yadda za su habbaka kasuwanci da kuma tattalin arzikin kasashen nasu.

Samar da kasafin kudin kungiyar na daga cikin abinda taron zai fi mayar da hankali kansa.

Mahalarta taron na da akidar cewa samar da masa'antu na daga cikin abinda zai karfafa kungiyar da kuma samarwa mutane aikin yi , kuma hakan zai taimawa kungiyar ci gaba da habakka.

A watan mayun 2018 ne Bankin bunkasa tattalin arziki na Brics ya dauki aniyar buda cibiyarsa a kasar Brazil a shekarar bana ,kamar yadda ya bude a kasar Afirka ta kudu.