Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutum 17 A Mali
A yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a Mali, rikicin kabilanci ya ci rayukan mutum 17 a tsakiyar kasar.
Rahotani daga kasar Mali na cewa a daren jiya juma'a wani rikicin kabilanci ya barke a kauyen Soumina dake kusa da garin Djenne na jahar Mopti dake tsakiyar kasar, lamarin da ya janyo asarar rayuka 17,kuma ya zuwa yamzu hukumomin kasar ba su yi karin haske ba kan abinda ya janyo wannan rikici.
Tawagar MDD a Kasar Ta Mali cikin wani rahoto da ta fitar na baya-bayan nan ta ce a shekarar 2018, kimanin fadace-fadace da rikcin kabilanci 100 ne ya gudana a cikin kasar da kuma ya yi sanadiyar salwanta rayukan mutane akalla 289.
Wannan tashin hankalin na zuwa ne a yayin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a gobe lahadi 29 ga wannan wata na yuli da muke ciki.
Tun a shekarar 2012 ne kasar Mali ta fada cikin rikici ,bayan juyin milki da sojojin kasar suka yi, sannan kuma 'yan tawayen abzunawan kasar da masu tsatsauran ra'ayin addini suka mamaye arewacin kasar.