Ana Zaben Shugaban Kasa A Mali
(last modified Sun, 29 Jul 2018 06:30:48 GMT )
Jul 29, 2018 06:30 UTC
  •  Ana Zaben Shugaban Kasa A Mali

A wannn lahadi Al’ummar kasar Mali za su gudanar da zaben shugabancin kasa cikin tsauraran matakan tsaro

Jami’an tsaro masu yawan gaske da suka hada da na kasar da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya ke gudanar da sintiri a sassa dabab daban na kasar domin tabbatar da cikakken tsaro yayin gudanar da zabe.

Akalla mutane miliyan takwas hukumar zaben kasar ta yi wa rijistar cancantar kada kuri’a a zaben wanda za a soma shi daga karfe 8 na safe agogon GMT zuwa 6 na yammacin wannan  rana  ta Lahadi.

Shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita da ke neman wa’adi na biyu, na fuskantar ‘yan takara sama da 24, sai dai daga cikinsu, ana ganin Souma’ila Cisse ne ke da karfin magoya bayan, da ya bashi dama zama abokin hamayya mafi girma ga shugaban kasar mai ci.

Zaben na Mali ya zo ne dai dai lokacin da kasar ke kokarin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi sassanta, kama daga na 'Yan ta’adda da kuma rikicin kabilanci, musamman a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, tsakanin mafarautan kabilun Bambara da Dogon kuma Fulani.