Tunusia : Jam'iyyar Annahdha Na Goyon Bayan Gwamnatin Shahid
(last modified Sun, 29 Jul 2018 11:52:05 GMT )
Jul 29, 2018 11:52 UTC
  • Tunusia : Jam'iyyar Annahdha Na Goyon Bayan Gwamnatin Shahid

Shugaban jam'iyyar Annahdha ta kasar Tunisia ya ce baya goyon bayan wargaza gwamnatin firai minista Yusuf Shahid don murabus dinsa zai kara yawan matsalolin kasar.

Kamfanin dillancin Labaran Anatoliyo ya nakalto Rashid Ghanushi shugaban jam'iyyar ta Annahdha yana fadar haka a jiya Asabar a wani taron magajin garuruwa na kasar a birnin Tunis. 

Ghanushi har ila yau ya bukaci Firai Ministan ya canza ministocin sa guda 6 don dai daita al-amura a gwamnatinsa. Sannan ya bukaci majalisar dokokin kasar ta amince da ministan cikin gida Hisham Fura'ii wanda firai miunistan ya gabatar mata. 

Jam'iyyar Annida mai mulki dai tana ganin Firai minista Yusuf Shahis ne ya jawo matsalolin da gwamnatin kasar take fama a halin yanzu, kuma da dama sun bukaci Yusuf Shahida ya ajiye aikinsa.