Yan Ta'adda Sun Kai Harin Rokoki A Arewacin Mali
(last modified Mon, 30 Jul 2018 06:52:48 GMT )
Jul 30, 2018 06:52 UTC
  • Yan Ta'adda Sun Kai Harin Rokoki A Arewacin Mali

Yan ta'adda a arewacin kasar Mali sun cilla makaman roka har sau 10 a kan garin Kidal a dai dai lokacinda ake zaben shugaban kasa a duk fadin kasar a jiya Lahadi.

Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa daya daga cikin rokokin ya fada kusa da wani rumfan zabe a cikin garin amma bai cutar da wani ba. 

A jiya Lahadi ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Mali inda yan takara 24 suka fafata a tsakaninsu, daya daga cikinsu macce ce, sannan shugaban kasa mai ci Ibrahim Kaita da Isma'ila Sice ne ake saran zasu zo kusa da juna a yawan kuri'un da aka kada. 

Tun shekara ta 2012 kasar Mali ta fada cikin tashe tashen hankula bayan da sojoji suka yiwa zabebben gwamnatinkasar Juyin mulki.