An Kai Hari A Yankin Arewacin Kasar Mali
(last modified Mon, 30 Jul 2018 12:12:01 GMT )
Jul 30, 2018 12:12 UTC
  • An Kai Hari A Yankin Arewacin Kasar Mali

Masu dauke da makamai sun kai hari da makaman roka a garin Kidal da ke arewacin kasar.

Daya daga cikin hare-haren sun sauka a kusa da inda ake gudanar da zabe, amma sai dai babu wanda ya jikkata

A jiya asabar ne dai aka yi zaben shugaban kasar wanda 'yan takara 24 suke gogayya da juna da mace guda daya.

Kasar Mali ta fuskanci juyin mulki a 2012, sannan kuma bullar kungiyoyi masu dauke da makmai da su ka hada da na 'yan ta'adda.

Majalisar Dinkin Duniya ta girke rundunar tabbatar da zaman lafiya wacce ake kira (MINUSMA.Haka nan sojojin kasar Faransa masu yawa suna girke a cikin kasar, sai dai hakan bai hana afkuwar kai hare-haren ta'addanci ba.