Somalia Da Eritrea Zasu Maido Da Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32552-somalia_da_eritrea_zasu_maido_da_huldar_diflomasiyya_tsakaninsu
Kasashen Eritrea da Somaliya sun cimma wata yarjejeniya yau Litini, ta mayar da huldar diflomatsiyya a tsakaninsu, da kuma tura jakadu a manyan biranen kasashen.
(last modified 2018-08-22T07:02:10+00:00 )
Jul 30, 2018 10:04 UTC
  •  Somalia Da Eritrea Zasu Maido Da Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu

Kasashen Eritrea da Somaliya sun cimma wata yarjejeniya yau Litini, ta mayar da huldar diflomatsiyya a tsakaninsu, da kuma tura jakadu a manyan biranen kasashen.

Wata sanarwa da gwamnatin Somalia ta fitar a yau, ta ce kasashen zasu maido da huldar diflomatiyya tsakaninsu, a wani mataki na kara dankon zumunci.

An dai sanya hannu kan wannan yarjejeniya ce tsakanin shugaban kasar Eritrea Issaias Afeworki, da kuma takwaransa na Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed.

Wannan yarjejeniyar dai ta kara fiddo yadda dangantaka ke samun samun karbuwa tsakanin kasashen yankin kahon Afrika, bayan wacce aka samu makwanni da suka gabata tsakanin kasashen Eritrea da kuma Habasha, wacce ita ce tra farko tun bayan samun 'yan cin kan kasar Eritrea a 1993.

Kafin hakan dai wadannan kasashen biyu sun shafe gomman shekaru basa jituwa, saboda zargin goyan bayan da gwamnatin Asmara ke wa mayakan Al'shabab dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida.