An Kai Hari Kan Mazabu Da Dama A Mali
Ma'aikatar cikin gidan kasar Mali ta sanar da cewa hare-hren da aka kai runfunan zabe da dama na kasar lamarin da ya janyo tarnaki a makomar zaben shugaban kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto ma'ikatar cikin gidan Mali a jiya Litinin na cewa hare-haren da aka kai runfunar zabe da kuma rikicin da aka yi a wasu yankuna ya janyo tarnaki a makomar zaben shugaban kasar.
Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce kimanin runfunar zabe 644 ne aka kasa gudanar da zabe har zuwa karshe lokacin da aka tanada saboda hare-haren da 'yan bindiga suka kai.
Har ila yau ma'aikatar cikin gidan Malin ta ce kashi 3% ne kacal na runfunar zabe ne kawai aka gudanar da zabe, aka kamala ba tare da matsala ba a kasar.
Kimanin Dakarun tsaro dubu 30 ne aka tanada domin tabbatar da tsaro a yayin zaben na kasar Mali da ya gudana a ranar 29 ga watan Yuli.