An bukaci Shugaban Kasar Afirka ta Kudu da ya yi murabus
'Yan Adawar Gwamnatin Afirka ta kudu ta bukaci shugaban kasar da ya sauka daga kan mukamin sa
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa A yau Juma'a 'yan adawar Gwamnatin Afirka ta kudu a Majalisar dokoki sun sanar da cewa za su dauki duk wani mataki domin sauke shugaba Jacob Zuma daga kan karagar milkin kasar.
A wani taron manema labarai da ya kira,Mamusi Mimany shugaban jam'iyar Adawa ta kasar A majalisar dokoki ya ce jam'iyarsa ba za ta kasance tare da Majalisar Zuma ba wajen kare da kuma gudanar da dokokin kasar.
Wannan kuwa na zuwa kwana guda bayan da kotu ta tabbatar da zargin da ake yi wa shugaba Zuma na yin amfani da kudade ba ta hanyar da ta dace wajen gyaran gidansa.
Kotun kundin tsarin milkin dai ta baiwa shugaba Zuma kwanaki 45 domin ya mutunta doka ya kuma mayar da kudaden da suka kai million 16 na dalar Amurka , domin kuwa a cewar kotun abin da ya yi na amfani da kuadden gwamnati wajen gyara wuraren da ba su da alaka da tsaro ya sabawa doka.
An bayyana cewa Shugaba Zuma ya yi amfani da wadannan kudade domin gyara wani gida mallakinsa.