Zimbabwe : Jagoran 'Yan Adawa Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32603-zimbabwe_jagoran_'yan_adawa_ya_yi_watsi_da_sakamakon_zabe
Jagoran 'yan adawa a Zimbabwe, Nelson Chamisa, ya yi wasti da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar ta sanar.
(last modified 2018-08-22T11:32:11+00:00 )
Aug 03, 2018 07:39 UTC
  • Zimbabwe : Jagoran 'Yan Adawa Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

Jagoran 'yan adawa a Zimbabwe, Nelson Chamisa, ya yi wasti da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar ta sanar.

Mista Chamisa, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya danganta sakamakon dana bogi, da kuma abun kunya ga hukumar zaben kasar ta ZEC.

 A cikin daren jiya Alhamis ne hukumar zaben Zimbabwen ta fitar da sakamakon da ya ayyana shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben tun zagayen farko da kashi 50,8% na yawan kuri'un da aka kada.