Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32604-za'a_je_zagaye_na_biyu_a_zaben_mali
A Mali, za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar, bayan da aka kasa samun dan takara da ya samu kason da ake bukata domin lashe zaben a tashin farko.
(last modified 2018-08-22T11:32:11+00:00 )
Aug 03, 2018 07:50 UTC
  • Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Mali

A Mali, za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar, bayan da aka kasa samun dan takara da ya samu kason da ake bukata domin lashe zaben a tashin farko.

Shugaban kasar mai ci Ibrahim Bubakar Keita ne ke sahun gaba a sakamakon zaben zagayen farko, saidai zai fafata da babban abokin hammayarsa Sumaila Cisse a zagaye na biyu.

A sakamakon da aka fitar jiya, Mista Keita, ya samu kashi 41,41% na kuri'un, a yayin da abokin takaransa M. Cisse ya samu kashi 17,80% na yawan kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi data gabata.