Somalia: Mutane Uku Suka Rasa Rayukansu Sanadiyar Fashewar Bam A Magadishu
Majiyoyin labarai daga birnin Magadishu na kasar Somalia sun bayyana cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom a kudancin birnin a yau Lahadi.
Tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar ta bayyana cewa tashin bom din ya auku ne a wani wurin bincike na sojoji a kudancin birnin.
Har'ila yau jaridar "Assomali Aljadeed" ta bayyana cewa mayakan Alshabab sun zartar da hukuncin kisa kan mutane ukku a garin Jilib na Lardin Juba daga kudancin kasar, daga ciki har da macce guda.
Tun shekara ta 2011 ne kungiyar yan ta'adda ta Alshabab wacce take aiki da kungiyar alqaeda suke iko da wasu sassa na kasar ta Somalia. Kokarin da sojojin gwamnati tare da na tarayyar Afrika da suke kokarin dawo da zaman lafiya a kasar ya kasa dawo da ikon gwamnati a duk fadin kasar.