Sojojin Najeriya Sun Ce Sun Kashe Akalla Yan Bindiga 20 A Zamfara
Akalla yan bindiga 20 suka mutu a lokacinda sojojin Nigeriya suka kai wa yan bindiga sumame a wurare daban daban a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto kakakin sojojin Kanar Mohammad Dole yana cewa a ci gaba da farmakin sharan Daji da sojojin kasar suka fara a jihar zamfara sun sami nasarar kashe yan ta'adda 20 sannan wasu kuma suka tsere daga raunuka a kananan hukumomin Tsafe da Zurmi.
Mohammad Dole yace sojojin sun yi kwanton bauna wa yan ta'addan a wani wuri da ake kira Dansadau inda suka saba bi a lokacinda suke kai hare hare kan mutane a kauyukan yankin. Ya ce sun kashe 20 daga cikinsu wasu sun tsira da raunuka sannan sun kona babura da dama.
Kakakin sojojin ya kara da cewa a cikin wadanda sojojin suka halaka sun hada da Bello Dankobo da Sani Maza wadanda suka shahara da kekashewar zuciya a hare haren da suke kaiwa mutanen yankin.
Mohammad Dole ya kammala da cewa aikin sojojin ya dawo da zaman lafiya a wadannan yankuna.