Shirin Rantsar da shugaban Nijer Mahamadou Issoufou
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3268-shirin_rantsar_da_shugaban_nijer_mahamadou_issoufou
Birnin Yamai ya fara karbar baki da za su halarci bikin rantsar da shugaban kasa a gobe Assabar
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 13:53 UTC
  • Shirin Rantsar da shugaban Nijer Mahamadou Issoufou

Birnin Yamai ya fara karbar baki da za su halarci bikin rantsar da shugaban kasa a gobe Assabar

A gobe Asabar ne ake shirin rantsar da Shugaba Issoufou Mahamadou domin ci gaba da mulki wa’adi na biyu a Jamhuriyar Nijar, bayan da ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar 20 ga watan Maris din da ya ghabata zagaye na biyu akan babban abokin adawarsa Hama Amadou, inda ya samu kashi 92,51% daga cikin kuri'un da aka kada a kasar . Yanzu haka dai ana ci gaba da shirye-shirye domin gudanar da gagarumin bikin rantsar da shugaban a birnin Yamai, baya ga haka birnin ya fara karbar bakuncin manya jami'an kasashen Afirka daga cikin su har da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Kieta.

Saidai za a gudanar da wannan biki ne ba tare da gungun Jam'iyun Adawa, inda suka yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana cewa daga ranar gobe 2 ga watan Avrilu, ba za su kalli shugaba Issoufou ba a matsayin shugaban kasar dake kan doka.