Sojojin Aljeriya Sun Rusa Wata Maboyar 'Yan Ta'adda A Yankin Arewacin Kasar
Rundunar sojin Aljeriya ta sanar da rusa wata maboyar 'yan ta'adda a lardin Aïn Defla da ke shiyar arewacin kasar.
Rundunar sojin Aljeriya ta sanar da cewa: A ci gaba da samamen da jami'an tsaron kasar ke gudanarwa a sassa daban daban na kasar da nufin tsarkake su daga gungun 'yan ta'adda, sun gano wata maboyar 'yan ta'adda a lardin Ain Defla da ke shiyar arewacin kasar da a cikin suka samu bama-bamai da ake harhada su da hannu da makaman yaki, inda suka dauki matakin lalata su.
Har ila yau majiyar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: A cikin kwanaki biyu da suka gabata, an gano wasu bama-bamai guda hudu a yankin arewa maso yammacin kasar tare da lalata su.
Tun bayan da jami'an tsaron Aljeriya suka fafata da wasu gungun 'yan ta'adda a yankunan da suke da tsaunuka a shiyar gabashin kasar, suka dauki matakin tsarkake yankunan kasar daga samuwar 'yan ta'adda.