An Zargi Gwamnatin Kasar Mali Da Kashe Fararen Hula
(last modified Fri, 10 Aug 2018 06:35:17 GMT )
Aug 10, 2018 06:35 UTC
  • An Zargi Gwamnatin Kasar Mali Da Kashe Fararen Hula

Majalisar Dinkin Duniya ce ta zargi sojojin na kasar Mali da kashe fararen hula da suka hada da wasu gwammai da sojojin gwamnati su ka yi wa kisan gilla ba bisa ka'ika ba.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya ci gaba da cewa; A tsakanin watannin Fabrairu da Yuli na wannan shekarar da aka gano wasu manyan kabarurruka a tsakiyar kasar, gwamnati ta yi furuci da kisan fararen hular.

Wani sashe na rahootn da kwararru su ka gabatarwa da kwamitin tsaro na Majalisar Dikin Duniyar sun bayyana cewa; A cikin hare-haren da jami'an tsaro suke kai wa da sunan yaki da ta'addanci suna tafka laifukan da su ke a matsayin take hakkin bil'adama.

Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun 2012 wanda kuma yake ci gaba har zuwa yanzu