An Kamala Yakin Neman Zabe Tsagaye Na Biyu A Mali
A Wannan Juma'a ce aka kawo karshen yakin neman zaben shugabancin kasa zagaye na biyu a Mali, inda ake shirin fafatawa tsakanin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Soumaila Cisse.
Yan takarar da suka zo a matsayin na uku da kuma hudu Aliou Diallo da Cheikh Modibo Diarra, kowanne ya bukaci magoya bayansa da su kada kuri’arsa ga wanda suke so, ba tare da kulla kawance da sauran ‘yan takara kamar yadda aka saba gani a siyasar kasar ba.
A makon da ya gabata ne Ministan kula da yankunan kasar, Mohammed Ag Erlafk ya shaidawa al’ummar kasar cewar, sakamakon zaben da akayi zagayen farko ya nuna cewar, shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya samu kusan kashi 42 na kuri’un da aka kada, yayin da Soumaila Cisse ya samu kusan kashi 18.
Sakamakon zaben na farko ya nuna cewar, dan kasuwa Aliou Diallo ya samu kusan kashi 8 na kuri’un da aka kada, yayin da tsohon ministan sufuri, Cheikh Modibo Diarra ya samu kashi sama da 7 da rabi.