An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu A Mali
Al'ummar kasar Mali sun gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a wannan lahadi, inda aka fafata tsakanin shugaba mai ci Ibrahim Boubakar Keita da abokin hamayarsa Soumaila Cise.
A wannan Lahadin ce al'ummar kasar Mali sama da miliyan takwas suka gudanar da zaben shugaban kasarsu a zagaye na biyu cikin tsauraran matakan tsaro don kaucewa kutse na 'yan ta'adda.
A zagayen farko na zaben, da aka yi a watan da ya gabata, shugaba Kieta ne ke kan gaba, bayan lashe kashi 41 na kuri'un da aka kada, yayinda Cisse ya samu kashi 18.
Sai dai kafin zaben na yau, a jiya Asabar, jami’an tsaron kasar ta Mali, sun bayyana samun nasarar wargaza wani shirin kaddamar da hare-haren ta’adanci a sassan Bamako babban birnin kasar, inda suka kame mutane 3.
Akalla jami’an sojin kasar dubu 36,000 ne aka baza cikin kasar domin tabbatar da tsaro inda aka fi mayar da hanakali kan yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, wanda ya fi fuskantar barazanar hare-hare da barkewar rikici.
Wasu daga jami’an sa ido kan zaben na Mali sun ce, yayin gudanar da zagayen farko na zaben shugabancin kasar, tashe tashen hankula sun tilasta rufe akalla kashi daya daga cikin biyar, na rumfunan zabe, a sassan kasar.