Tashin Nakiya Ya Hallaka Mutum 6 A Gabashin Burkina Faso
(last modified Sun, 12 Aug 2018 18:59:26 GMT )
Aug 12, 2018 18:59 UTC
  • Tashin Nakiya Ya Hallaka Mutum 6 A Gabashin Burkina Faso

Akalla Mutum 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin nakiya a gabashin kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto majiyar tsaron kasar Burkina Faso na cewa a daren jiya asabar wata nakiya da aka dasa kan hanyar mota ta tashin da wata motar jami'an tsaro a gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar sojoji 5 da kuma wani farar hula guda.

Har ila yau rahoton ya ce tashin nakiyar ya janyo hasarar dukiya baya ga asarar rayukan da aka samu.

Tun daga shekarar 2015 ne kasar Burkina Faso ta fada cikin matsalar tsaro, inda daga wancan lokaci zuwa yanzu kasar ta fuskanci hare-haren ta'addanci a yankunan arewa, tsakiya da kuma gabashin kasar.