Al'ummar Tunisiya Sun Gudabar Da Zanga-Zangar A Gaban Ofishin Jakadancin Saudiya
Wasu daga cikin al'ummar kasar Tunisiya sun gudanar da jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Saudiya dake birin Tunis domin nuna rashin amincewarsu kan hana visa
Tashar Talabijin din Aljazera ta habarta cewa daga makoni biyu da suka gabata zuwa yanzu, masu adawa da siyasar ma'aikatan ofishin jakadancin na Saudiya ke taruwa a gaban ofishin domin nuna rashin amincewarsu na hana visa na gudanar da aikin hajji.
Masu zanga-zangar na cewa ma'aikatan ofishin jakadancin na Saudiya sun yi burus da bukatar 'yan kasar na basu Visar hajjin, sannan kuma suna daukan kason su suna sayarwa 'yan kasar Libiya da ma wasu kamfanoni na jigilar alhazai, sun mayar da visar abin kasuwanci.
Saidai Ofishin jakadancin na Saudiya dake birnin Tunis ya ki cewa komai game da wannan zargi.