Madugun 'Yan Adawar Kasar Mali Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe
Dan takarar jami'iyyar adawa Soumaila Cisse ya ce al'ummar Kasar Mali ba za su lamince da murdiyar zabe ba, don haka al'umma "su tashi tsaye".
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Jagoran 'yan adawa na kasar Mali Soumaila Cisse a jiya Litinin na cewa ba zai amince da sakamakon zabe zagaye na biyu da aka yi a kasar wanda ya ce cike yake da magudi, ya kuma yi kira ga al'ummar kasar "da su tashi tsaye".
Cisse ya ce su nada dalilai dake tabbatar an aikata magudi a zaben don haka ba za su amince da sakamakon ba.
Madugun 'yan adawar ya bayyana haka ne ga taron manema labarai a hedikwatar jam'iyyarsa da ke birnin Bamako.
Ya ce al'ummar Mali ba za su lamunci murdiyar zabe ta masu mulkin kama karya ba.