Aug 15, 2018 06:38 UTC
  • Guterres ya bukaci 'yan takarar zaben Mali su kai zuciya nesa

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai sun bukaci taka tsan tsan a Mali, bayan da dan takaran zaben shugaban kasa daga bangaren yan adawa, Soumaila Cisse ya ce ba zai amince da sakamakon zaben kasar ba

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto babban saktare janar na MDD  Antonio Guterres na cewa ya kamata al'ummar kasar Mali su kwantar da hankalinsu  har zuwa lokacin da za’a bada kammalallen sakamakon zaben, yayin da kungiyar kasashen Turai ta bukaci bangarorin da su kaucewa bayyana sakamakon na kashin kan su.

Guterres ya bukaci bangarorin siyasar kasar da su kai zuciya nesa, su kuma kuji firta kalaman da za su tayar da fitina a kasar

Tuni dai jagoran 'yan  adawa na kasar Mali Soumaila Cisse a jiya Litinin na  cewa ba zai amince da sakamakon zabe zagaye na biyu da aka yi a kasar wanda ya ce cike yake da magudi, ya kuma yi kira ga al'ummar kasar "da su tashi tsaye".

Cisse ya ce akwai  dalilai dake tabbatar an tabka magudi a zaben don haka ba za su amince da sakamakon ba.

Tags