An Hana Amfani Da Kayan Amurka Cikin Kasar Senegal
(last modified Wed, 15 Aug 2018 12:46:08 GMT )
Aug 15, 2018 12:46 UTC
  • An Hana  Amfani Da Kayan Amurka Cikin Kasar Senegal

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ba da labarin cewa; Mutanen kasar ta Sengal sun fara kamfe na hana amfani da kayan da Amurka ta kera

A cikin birane da dama na kasar ta Senegal an fara gudanar da kiran a kaurace wa kayan da aka kera a Amurka domin nuna kin amincewa da siyasar kasar.

Masu gudanar da kamfe din suna bijiro da kayan da aka kera a kasar Turkiya a matsayin wadanda za su maye gurbin na Amurka a kasuwannin kasar ta Senegal.

Kasar Amurka ta kakaba wa wasu jami'an kasar Turkiya takunkumi kamar kuma yadda da sanya kudin fito masu yawa akan karafan da kasar take saya daga Turkiya.

Gwamnati da al'ummar kasar Turkiya suna zargin Amurka da kokarin raunana tattalin arzikin kasar tasu