Aug 30, 2018 06:23 UTC
  • Waziriyar Kasar Jamus Ta Fara Ziyara Aiki A Wasu Kasashen Yammacin Afrika

Waziriyar Kasar Jamus Angela Michel ta fara wani ziyarar aiki a wasu kasashen Afrika a jiya Laraba.

Tashar radiyo" Duch Welle" muryar jam'ar Jamus ta bada sanarwan cewa Angela Michel zata ziyarci kasashen Ghana Najeriya da kuma Senegal a wannan tafiyar don tattauna batutuwan tattalin arziki. Amma masana da dama suna ganin zata tattauna batun bakin haure daga wadannan kasashe ukku da suke samun mafaka a kasar Jamus, don dawo da su gida. 

Wasu masana sun bayyana cewa akwai yan gudun hijira kimani dubu 11 wadanda suke samun mafata a kasar Jamus tun shekara ta 2017. Kuma dukkaninsu sun fito ne daga wadannan kasashen ukku wato Najeria Ghana da kuma Senegal.

Don haka ana saran Angela Michel za ta nemi hadin kai daga wadannan kasashen don maida yan gudun hijirar kasashensu.  

Tags