Kasar Algeria Tana Goyon Bayan Iran A Rigimar Da Take Da Amurka
Lawize Hanun sakataren jam'iyyar ma'aikata a kasar Algeria ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa tana goyon bayann Iran a rigimar da take da kasar ta Amirka.
Majiyar muruyar JIM ta nakalto Hanun yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Algeria tana goyon bayan kasar Iran da kuma kungiyarHizbullah ta kasar Lebanon sannan ba ta yarda da sanya kungiyar hizbullah a cikin jerin sunayen yan ta'adda a duniya ba.
Dangane da yakin da kasar saudia take jagoranta a kasar Yemen kuma sakataren jam'iyyatar ta ma'aikata ya yi allawadai da shi ya kuma bayyana cewa Saudia tana wakiltan Amurka a yakin
Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne sojojin kawance kasashen larabawa suna fara kaiwa mutanen kasar yemen hare hare, wanda ya zuwa yanzo an kashe mutane kimani dubu 4 sannan dubban dadruruwa suka ji rauni a yayinda miliyoyu suka zama yan gudan hijira.