Afirka Ta Kudu: An Kashe Yan Kasashen Waje 4
"Yansandan Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa; Sabon fadan da ya barke a tsakanin yan kasa da bakin haure ya ci rayukan mutane 4
Kamfanin dillancin labarun Faransa da ya nakalto majiyar 'yan sandan kasar suna cewa; An yi fadan ne a tsakanin 'yan kasar da kuma bakin haure a yankin Soweto.
Fadan ya barke ne bayan samun gawar wani dan kasar ta Afirka ta Kudu a wannan yakin, wanda kuma aka danganta shi ga 'yan kasar waje.
'Yan sanda sun sanar da kame mutane 27 da su ka hada da wata mace guda daya.
Majiyar 'yan sandan ta ce dukkanin wadanda aka kashe din 'yan kasar waje ne.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun fada a tsakanin 'yan kasar Afirka ta kudu da bakin haure mazauna kasar. A baya fadan ya yi sanadin cin rayukan mutane da dama sanadiyyar fadan.