Bom Ya Tashi A Babban Birnin Kasar Somaliya Magadishu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33012-bom_ya_tashi_a_babban_birnin_kasar_somaliya_magadishu
A kalla mutane 3 ne su ka mutu sanadiyyar tashin bom din a birnin Magadishu
(last modified 2018-09-02T11:04:52+00:00 )
Sep 02, 2018 11:04 UTC
  • Bom Ya Tashi A Babban Birnin Kasar Somaliya Magadishu

A kalla mutane 3 ne su ka mutu sanadiyyar tashin bom din a birnin Magadishu

Bom din dai an dasa shi ne a cikin wata mota a kudancin birnin wanda ta kashe fararen hula da kuma jikkata wasu da dama.

Kungiyar al-shabab ta kasar ta dauki nauyin kai harin.

Tun a 2011 ne dai kasar ta Somaliya take fada da hare-haren ta'addanci na kungiyar al-shabab.

Sai dai sojojin kasar ta Somaliya sun sami nasarori masu yawa akan 'yan ta'addar tare da kwace yankunan da su ka shimfida iko a cikinsu a baya.

Kungiyar al-Shabab tana a matsayin babbar barazana ta tsaro ga gwamnatin kasar da kuma kasashen makwabta da take kai wa hare-hare.