An Fara Taro Kan Kasar Siriya A Birnin Ganeva
Manzon Musaman na MDD kan Kasar Siriya ya fara tattaunawa da wakilan kasashen Rasha da Iran gami da Turkiya a Hedkwatar Majalisar dake birnin Ganeva.
A yammacin wannan talala ce manzon musaman na MDD kan kasar Siriya Stéphane Dujarric ya fara ganawa da wakilan kasashen Rasha, da Iran da Turkiya domin neman shawarwari kan yadda za a kafa kwamitin da zai sabunta dokokin kasar Siriya.
Bayan haka, taron zai tattauna kan yadda za a tabbatar da sulhu tsakanin al'ummar kasar ta Siriya.
A yayin barinsa birnin Tehran, wakilin kasar Iran Jabir Ansari ya bayyana cewa, bayan tattaunawar da wakilin MDD, zai gana da tawagar kasashen Rasha da Turkiya a kebance.
Idan ba a manta dai tun a watan janairun 2017 ne jamhoriyar musulinci ta Iran tare da hadin kan kasashen Rasha da Turkiya ta fara shirya taro da nufin tabbatar da sulhu a kasar Siriya.