Muftin Kasar Uganda Ya Soki Gwamnatin kasar Kan Siyasar Wariya
(last modified Tue, 11 Sep 2018 19:08:17 GMT )
Sep 11, 2018 19:08 UTC
  • Muftin Kasar Uganda Ya Soki Gwamnatin kasar Kan Siyasar Wariya

Mai bayar da fatawa na kasar Uganda ya soki gwamnatin kasar kan yadda take nunawa Al'ummar musulmi babbanci a kasar, inda ya bukaci gawanmatin kasar ta gyara siyasarta ta kuma kiyaye adalci tsakanin mabiya addinan kasar

Yayin da yake gabatar da jawabi a wurin jana'izar wani babban jam'in sojan kasar musulmi mai suna Kanal Muhammad  Kirumira, Sheikh Shaban Ramadhan Mubaje baban mufti na kasar Uganda ya nemi gwamnatin kasar da ta gaggauta canza siyasar wariya da take nuna al'ummar musulmi a kasar, sannan ya bukaci gwamnati da tattabar da adalci tsakanin mabiya addinan kasar.

Kwanaki uku da suka gabata ne wasu 'yan bindiga suka yiwa  kanal Muhammad Kirumira kisan gilla.

Wannan lamari na zuwa ne bayan wani jawabi da Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya yi a ranar lahadi 9 ga watan Satumba, inda ya zargin kasashen waje da yin katsa landan a harakokin cikin gida na kasar  da kuma kokarin samar da rikicin siyasa a kasar, sannan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauki kwararen matakan tsaro da nufin ganin masu kokarin tayar da rikici ba su nasara ba.