Mutanen Kasar Siriya Suna Zaben Yan Majalisar Lardunan Kasar A Yau Lahadi
(last modified Sun, 16 Sep 2018 19:05:12 GMT )
Sep 16, 2018 19:05 UTC
  • Mutanen Kasar Siriya Suna Zaben Yan Majalisar Lardunan Kasar A Yau Lahadi

A safiyar yau Lahadi ce aka fara zaben majalisun larduna a kasar Siriya wanda yake nuna cewa an koma ga tsarin democradiya da gaske a kasar.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar ta Siriya ya bayyana cewa a zaben yau lahadi yan takara kimani dubu 40 ne suke neman cike kujeru 18,478 na majalisun lardunan kasar. 

SANA ya kara da cewa an bude rumfunan zabe da misalin karfe 7 na safi kuma fitar mutane a birnin Damascus babban birnin kasar yana da yawa. Khadija Al-Hosshan shugaban hukumar zabe a zaben lardunan kasar a babban birnin kasar ta shaidawa masa cewa zaben majalisun lardunan kasar shi ne zai bawa mutane damar tabbatar da cewa su ne suke iko da kasa don wakilansu da suka zaba ne zasu gudanar da ayyukan ci gaba a yankunansu.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar Siria ta bayyana cewa kasar tana da mazamu 88 ne, sannan an kafa rumfunan zabe har dubu 6,551. Sannan hukumar zabe tana da damar kara lokacin kada kuri'a har zuwa sa'o'i 5, idan ta ga ya dace.