Najeriya: Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan Kungiyar Boko Haram 3
(last modified Mon, 17 Sep 2018 13:04:56 GMT )
Sep 17, 2018 13:04 UTC
  • Najeriya: Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan Kungiyar Boko Haram 3

A jiya Lahadi ne sojojin kasar ta Najeriya su ka sanar da kashe 'yan kungiyar ta Boko Haram 3 a yankin arewa maso gabashin kasar

Kisan 'yan kungiyar ta Boko Haram, ya zo ne bayan wani harin kwanton bauna da suka yi wa sojojin Najeriya.

A cikin watannin bayan nan kungiyar ta Boko Haram ta kai munanan hare-hare akan sojojin gwamnatin kasar  tare da kashe da dama daga cikinsu.

Tun a 2009 ne dai Sojojin kasar ta Najeriya suke kalubalantar hare-haren ta'addanci kungiyar Boko Haram wnada kawo ya zuwa yanzu sun ci rayukan mutane 20,000 sannan kuma wasu mutane miliyan biyu su ka zama 'yan gudun hijira.

A 2015 ne shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar al-Bagadadi ya yi wa kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS mubayaa.