Shugaban Aljeriya Ya Yiwa Bangaren Tsaron Kasar Garan Bawul
Shugaban kasar Aljeriya ya sauke manyan hafsan sojojin kasar daga kan mikaminsu
Shugaban kasar Aljeriya Abdul Aziz Bouteflika ya sauke Major General Ahsan Tafir Babban hafsan rundunar sojojin kasa ta kasar, da Major General Abdul-kader Lunas babban hafsan rundunar sojojin sama ta kasar.
Rahoton ya ce Shugaba Boutefilka ya nada Major General Saeed Shankarihah a matsayin babban hafsan sojojin kasa, sannan kuma ya nada Major General Bou Ma'azah Muhamad a matsayin babban hafsan rundunar sojojin sama na kasar, har ila yau ya nada Major General Garis Abdul-hamid a matsayin sabon saktare janar na ma'aikatar tsaron kasar.
A bangare guda kuma shuganan kasar ta Aljeriya ya sauke shugaban hukumar tsaron kasar Muhamad Tayyar da shuganan tsaron filin sauka da tashi na jiragen saman kasar Hawari Bou madin daga kan mikaminsu, saboka sun taimakawa tsohon kwamandan sojojin kasar da suka yi na ficewa daga cikin kasar zuwa Faransa bayan da sun san cewa kotu ta hana shi fita daga cikin kasar.
Wannan garan bawul na zuwa ne a yayin da kasar ta Aljeriya ke shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2019.