Sep 19, 2018 15:06 UTC
  • Biritaniya Ta Soke Tallafin Da Take Baiwa Zambiya

Gwamnatin Biritaniya ta sanar da soke tallafin da take baiwa Zambiya, bayan da gwamnatin Zambiyar ta tabbatar da bacewar Dala Miliyan 4,3 na tallafin da Biritaniyar ke baiwa marasa galihu na Zambiya.

Biritaniya ta ce ta dau matakin ne bayan bankado zargin cin hanci da rashawa a cikin gwamnatin Shugaba Edgar Lungu na Zambiya.

Kudaden dai na shirin nan ne na Biritaniya dake tamaikawa masu karamin hali a kasar ta Zambiya, inda sama da kashi 50% na al'ummar kasar Miliya 17 ke rayuwa a cikin talauci.

Shirin dai na taimakawa bangaren Ilimi da kiwan lafiya da kuma abinci mai gina jiki, da kuma aikewa da kudade ga 'yan Zambiyar masu fama da matsanancin talauci.

Ko baya ga Birtaniya ma, kasashen da suka hada da Ireland, Finland da Sweden sun sanar da soke tallafin da suke baiwa kasar ta Zambiya, a yayin da asusun bada lamuni na duniya IMF shi ma ya sanar da soke bashin da yake baiwa kasar, saboda fargabar da yake da ita.

 

Tags