An Haramta Zurga-zurga Babura A Gabashin Burkina Faso
Hukumomi a Burkina faso sun haramta zurga-zurga ta babura da kuma a daidaita sahu a yankin gabashin kasar, inda tun watan Agusta da ya gabata fararen hula da dama da kuma jami'an tsaro suka rasa rayukansu, sakamakom hare haren 'yan bindiga.
Wata sanarwa da gwamnan yankin Kanal Usman Tarore ya sanya wa hannu, ta ce an haramta wa babura da kuma 'yan a daidaita sahu zurga zurga daga karfe bakwai na yamma har zuwa biyar na safe a yankin, daga ranar 18 ga watan Satumba nan har sai abunda hali ya yi.
Su kuwa motocin dakon kaya dana sufirin al'umma suna da izinin yin zurga zurga, amma za'a dinga yi masu bincike mai zurfi.
Sanarwar ta kuma bukaci masu aikin harkar zinari ba bisa ka'ida ba a yankin dasu fice daga wuraren, kana su kuwa mafarauta dake cikin jeji a yankin an basu wa'adin sa'o'i 24 su bar wajajen.
Wannan matakin dai na daga cikin alkawarin da shugaban kasar, Roch Marc Christian Kaboré, ya dauka na dakile hare haren ta'addancin da ake kaiwa a yankin gabashin kasar.
Kimanin mutane talatin ne fararen hula da sojoji ne aka kashe a yankin a tsakanin ranakun 28 ga watan Agusta zuwa 15 ga watam Satumban nan.