An Sace Wasu 'Yan Kasashen Waje A Burkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33316-an_sace_wasu_'yan_kasashen_waje_a_burkina_faso
Rasohanni daga Burkina Faso na cewa an sace wasu 'yan kasashen waje uku dake aiki a yankin Inata dake arewa maso yammacin kasar
(last modified 2018-09-24T07:34:46+00:00 )
Sep 24, 2018 07:34 UTC
  • An Sace Wasu 'Yan Kasashen Waje A Burkina Faso

Rasohanni daga Burkina Faso na cewa an sace wasu 'yan kasashen waje uku dake aiki a yankin Inata dake arewa maso yammacin kasar

Mutanen uku sun hada da Ba'indiye guda da wani dan Afrika ta Kudu da kuma wani dan kasar ta Burkina Faso.

Dukkan dai mutanan ma'aikatan wata mahakar zinari ce dake yankin na Inata.

Bayanai dai sun ce wasu 'yan bindiga ne da ba'a tantance ko suwa ne ba suka sace mutanen kan hanyar Inata zuwa Djibo.