Afirka Ta Kudu Ta Karyata Mayar Da Jakadanta Zuwa Tel Aviv
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta kudu a wani bayani da ta fitar tana cewa; Jakadanta a A Tel Aviv Sisa Ngombane, ya je gudanar da wasu ayyukansa ne na kashin kansa ba aiki ya koma ba
Bayanin ya ci gaba da cewa da zazar jakadan ya gama abin ya kai shi zai sake komawa Afirka ta kudu.
Wani sashe na bayanin ya ce; Dalilin da ya sa Afirka ta kudu ta janye jakadanta daga haramtacciyar kasar Isra'ila yana nan bai sauya ba.
Tun da fari kafafen watsa labarun haramtacciyar kasar Isra'ila sun watsa labarin dake cewa; jakada Sisa ya koma bakin aiki.
Kasar Afirka Ta Kudu ta janye jakadanta ne daga Tel Aviv bisa abin da ta kira amfani da karfi da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi akan al'ummar palasdinu, musamman mutanen zirin Gaza.
Al'ummar Gaza suna gudanar da Zanga-zanga a kowace juma'a domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da takukunin da aka kakabawa yankin. Kawo ya zuwa yanzu palasdinawa da dama ne su ka yi shahada sanadiyyar wutar da sojojin sahayoniya suke bude musu.