Shugaban Mali Ya Bukaci Taimakon Kungiyoyin Kasa Da kasa
Shugaban kasar Mali ya bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa na tabbatar da tsaro a kasar da ma yankin Sahel gaba daya.
A yayin gabatar da jawabinsa a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 dake gudana a birnin New York na kasar Amurka, Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su taimakwa gwamnatinsa wajen zartar da yarjejjeniyar sulhun da a aka cimma tare da kungiyoyin 'yan tawayen kasar.
Yayin da yake ishara kan ci gaban da aka samu na zartar da yarjejjeniyar sulhun, Shugaban kasar Mali ya ce dan abinda ke hanun gwamnati ba zai bata damar zartar da dukkanin yarjejjeniyar sulhun da aka cimma a kasar.
A yayin wannan zama a kwai babban saktare na MDD Antonio Guterres da ministocin harakokin wajen kasashen Nijer, Aljeriya da Faransa da kuma shugabanin kwamitocin kungiyar tarayyar Afirka da wakilan kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da Babbar jami'a mai kula da siyasar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini.
A nasa bangare Babban saktare janar na MDD ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su yi iya kokari na ganin sun taimakawa kasar ta Mali da ma kasashen yankin sahel domin magance matsalar tsaro da suke fuskanta.