Ambaliya Ruwa Ta Ci Rayukan Mutum 200 A Najeriya
(last modified Thu, 27 Sep 2018 19:24:05 GMT )
Sep 27, 2018 19:24 UTC
  • Ambaliya Ruwa Ta Ci Rayukan Mutum 200 A Najeriya

Hukumomin Najeriya sun sanar da mutuwar mutum 200 biyo bayan ambaliyar ruwa a yankuna daban daban na kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan alhamis, gwamnatin Najeriya ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara a shekarar bana ya janyo ambaliya ruwa a jahohi 12 na kasar, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan mutane kimani 200 tare da raba wasu dabai da mahalinsu.

Rahoton ya ce yawan ruwan sama da aka samu a bama ya sanya kogin Niger da na Benue cika da batsewa har ta kai suka janyo ambaliyar ruwa a kauyukan dake kewayensu, inda duban mutane na kauyukan suka gudu, wasu kuma ambaliyar ruwa ya ritsa da su.

Kwanakin goma da suka gabata an sanar da dokar ta bace a jahohin Kogi, Niger-Delta, da Anambara sanadiyar ambaliyar ruwan.

Jahar Kogi ke na tsakiya Najeriya ne yayin da jahohin Niger-Delta da Anambara ke kudancin kasar, tuni dai kunigyar kai agaji ta kasar ta yi gargadin billar cutar kwalara da awadannan yankuna.

Bisa wani rahoto da MDD ta fitar, kimanin mutuane 100 ne suka rasa rayukansu sanadiyar billar cutar kwalara a kudancin Najeriya makoni biyu da suka gabata.